18 Oktoba 2026 - 08:39
Source: ABNA24
Kabul: Akwai Hatsarin Ruftawar Dutsen Da Ke Saman Mazauna "Chehelston" + Hotuna

Kusan gidaje 300 a yankin Chehelston da ke kudancin Kabul suna cikin haɗarin zamewar ƙasa da faɗuwar duwatsu, bayan da manyan tsage-tsage suka bayyana a dutsen da ke fuskantar gidajensu. Tsage-tsagen sun kai tsawon mita 150 zuwa 300, kuma faɗin wasu ya kai mita 3 zuwa 4.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Mazauna sun danganta matsalar da hakar duwatsu da aka yi shekaru da yawa daga gangaren, wanda ya bar wasu sassan dutsen babu komai. Hukumomi sun dakatar da ayyukan hakar, kuma hukumar kulawa hatsarurruka ta aika ƙwararru don ganin yanayin haɗarin. An gargadi mazauna su nisanta daga wuraren da ake yiwuwar zamewa, kuma yanke shawara kan ficewa daga wurin ya dogara da sakamakon bincike.

Ƙwararrun masana sun ce bai kamata a takaita dalilin ga hakar duwatsu kawai ba, tana iya kasancewa sakamakon haɗuwar abubuwa na halitta da na ɗan'adam kamar ɗebo ruwan ƙasa da nauyin gine-gine. Haɗarin ya kuma shafi Hasumiyar Chehelston, wani ginin tarihi da ke kusa.

Babbar matsalar da ke ƙara wahalar ficewa da kwashe kaya ita ce rikicin gidaje a Kabul: yawancin iyalai ba su da kuɗin hayar wani gida ko kuɗaɗen ƙaura, musamman bayan ƙaruwar buƙatar gidaje sakamakon komawar 'yan gudun hijira daga Iran da Pakistan. Mazauna suna kira ga hukumomi da su samar da mafita ta zaɓin wurin zama, ba iya gargadi kawai ba.

…………..

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha